Nigeria : Janye gayyatar da NBA ta yiwa Elrufai: Yan Shi'a mabiya Zakzaky sun yi farin ciki
on 2020/8/22 13:42:13
Nigeria

Click to see original Image in a new window
Kungiyar ‘yan uwa Musulmai ta Shi’a wacce aka fi sani da IMN ta jinjina wa matakin janye gayyatar da kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai domin ya yi jawabi a babban taronta da za a gudanar.


Kungiyar lauyoyin ta dai janye gayyatar da ta yi wa El-Rufai ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta, bayan zanga-zangar da wasu lauyoyi suka gudanar kan hakan. A wani sako da kungiyar lauyoyin ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa ta sanar da gwamnan matakinta na janye gayyatar da ta yi masa zuwa wajen taronta. Ta ce ta yi hakan ne sakamakon koken wasu mambobinta da ke zargin gwamnan da gazawa wajen shawo kan rikicin Kudancin Kaduna da kuma take hakkin al’umma.
Janye gayyatar da NBA ta yiwa Elrufai: Yan Shi'a mabiya Zakzaky sun yi farin ciki Hoto: PM News Source: UGC Kungiyar Shi’a a cikin wata sanarwa daga kakakinta, Ibrahim Musa, a ranar Juma’a ta bayyana cewa gwamnan bai cancanci halartan taron ba, sashin Hausa na BBC ya ruwaito. A gefe guda kuma, mun ji cewa El-Rufa'i ya bayyana janye gayyatar da kungiyar lauyoyin Najeriya, ta yi masa a matsayin mai jawabi a wurin taron ta da 'rungumar rashin adalci'. A cikin sanarwar da mai magana da yawun sa, Muyiwa Adeleke, ya fitar a madadinsa a ranar Alhamis, ya ce El-Rufai zai cigaba da yin tsokaci a kan batutuwan da ya ke ganin za su kawo cigaba a kasar duk da janye gayyatar.
"Duk da cewa NBA ce ke da ikon zabar wanda zai yi jawabi a wurin taron ta, Malam El-Rufai yana son a sani cewa dama ba shi ya nemi a gayyace shi ba kuma janyewar ba za ta rage shi da komai ba," in ji sanarwar. "Ga ƙungiyar da ya dace ta rika bawa adalci muhimmanci, abin mamaki ne yadda ta yanke hukunci a kan al'amarin ba tare da jin ta bakin bangarorin biyu ba. Yadda suka bari matsin lamba ya canja musu ra'ayi alama ce da nuna sun rungumi rashin adalci da rashin bin doka." Gwamnan ya ce zai mayar da martani a kan bata masa suna da aka yi a lokacin da ya sace cikin takardar ƙorafin da aka shigar a kansa.

Previous article - Next article Printer Friendly Page Send this Story to a Friend Create a PDF from the article


Other articles
2023/7/22 15:36:35 - Uncertainty looms as negotiations on the US-Kenya trade agreement proceeds without a timetable
2023/7/22 13:48:23 - 40 More Countries Want to Join BRICS, Says South Africa
2023/7/18 13:25:04 - South Africa’s Putin problem just got a lot more messy
2023/7/18 13:17:58 - Too Much Noise Over Russia’s Influence In Africa – OpEd
2023/7/18 11:15:08 - Lagos now most expensive state in Nigeria
2023/7/18 10:43:40 - Nigeria Customs Intercepts Arms, Ammunition From US
2023/7/17 16:07:56 - Minister Eli Cohen: Nairobi visit has regional and strategic importance
2023/7/17 16:01:56 - Ruto Outlines Roadmap for Africa to Rival First World Countries
2023/7/17 15:47:30 - African heads of state arrive in Kenya for key meeting
2023/7/12 15:51:54 - Kenya, Iran sign five MoUs as Ruto rolls out red carpet for Raisi
2023/7/12 15:46:35 - Ambassador-at-Large for Global Women’s Issues Gupta Travels to Kenya and Rwanda
2023/7/2 14:57:52 - We Will Protect Water Catchments
2023/7/2 14:53:49 - Kenya records slight improvement in global peace ranking
2023/7/2 13:33:37 - South Sudan, South Africa forge joint efforts for peace in Sudan
2023/7/2 12:08:02 - Tinubu Ready To Assume Leadership Role In Africa
2023/7/2 10:50:34 - CDP ranks Nigeria, others low in zero-emission race
2023/6/19 15:30:00 - South Africa's Ramaphosa tells Putin Ukraine war must end
2023/6/17 15:30:20 - World Bank approves Sh45bn for Kenya Urban Programme
2023/6/17 15:25:47 - Sudan's military govt rejects Kenyan President Ruto as chief peace negotiatorThe Sudanese military government of Abdel Fattah al-Burhan has rejected Kenyan President William Ruto's leadership of the "Troika on Sudan."
2023/6/17 15:21:15 - Kenya Sells Record 2.2m Tonnes of Carbon Credits to Saudi Firms

The comments are owned by the author. We aren't responsible for their content.